A mafi yawancin lokutan mukan yi korafin cewar bamu da kudi sannan bamu da hanyar da zamu sameta, wadda a hakikanin gaskiya bamu san wasu ba wasun kuma bamu jarrabasu bane. Sanin kowa ne dai a halin yanzu kusan ko wani daya daga cikin mu na mu’amala da kafar sadarwa ta yanar gizo (Internet) musamman dandalin sadarwa na zamani.
Mafi yawancin wadannan mune wato matasa yan uwana, mukan bata kusan dukkan lokutanmu ne wajen yin chatting, karanta labaran kwallo, neman yan mata, karanta littatafan hausa na soyayya ko yaki, neman saurayi, karatun boko, kallon videon kwallo, wakar hausa ko misic da dai makamantansu. Wannan shine abin da ya shagaltar da mu har ma ya sanya bamu kula da wasu manyan damammaki da zasu iya amfanemu domin samawa kanmu wasu ‘yan kudade na a kasha, wasu lokutan ma har yakan shagaltar damu wajen yin ibada.
A zamanin da muke ciki yanzu mutane sunfi sha’awar aikin gwamnati mutum yana so aji ana cewa ya tafi office ko kuma yana da hadadden office mai dauke da kayan sanyi na zamani sannan kuma a karshen wata yana da wani kayataccen albashi mai tsoka da wannan ake rudan wasu sannan a cusa musu sha’awar shigarta ta ko wacce hanya.
Idan kuma muka maida duba izuwa ga sana’ar hannu zamu ga cewar akwai wasu sana’oi da dama da mutum
zayyi wanda zai iya tashi da dubu 5 koma fiye da haka wadda in an kwatanta za’a ga cewa abinda mutum zai samu a karshen wata zai nikka albashir mai aikin gwamnati har sau biyu ko fiye da hakan.
Wani abin mamaki ma shine kusan ko wane matashi sai ya yi wani sana’a kafin ya iya samun kudin da zai siya Data, amma kuma bai san ta yaya zai iya samin kudin a saman yanar gizo (Internet).ta hanyar amfani da datar daya siya. Insha Allahu a wannan makon, Fasahabloq zata kawo muku wadansu cikakkun hanyoyin da za’a iya bi domin neman na kashewa a saman yanar gizo (Internet).
0 Comments