Ticker

6/recent/ticker-posts

MENENE GRAPHIC DESIGN

Graphic Design zane ne da ake tsara shi ta hanyar hada rubutu (text) da siffofi (shapes) da kuma hotuna (pictures), a tsara su ayi musu kwalliya don su bada launi mai kyau.




A misalan Graphic Design sune kamar:

zana logo, I'd card, invitation card, certificate, poster, flyer da dai sauran su, zana wadannan abubuwa shi ake kira da Graphic Design Wannan abu wato Graphic design Abu ne da mutane suke matukar bukatar shi, saboda yawanci mutane idan za suyi wani biki ko taro ana yi musu invitation na wannan taron da za su yi domin a rabawa mutane, haka ma masu sana'a ana yi musu logo na kasuwancin su ko kuma poster ta tallata kayan da suke siyarwa, a takaice dai Graphic design abu ne da ake da bukatarsa.

Mafi yawan mutane suna da ra'ayi tare da bu'katar koyan ilimin graphic design amma rashin damar mallakar computer da basu dashi ya hanasu yun'kurin neman ilimin graphic design. Idan kana daga cikin irinsu tsaya kaji...

Cigaban da duniya take samu a 6angaren ilimin technology akwai gudunmuwa babba wadda graphic designers suke badawa ta 'bangarori bila'adadin, hakan yasa aka samar da wasu manhajoji na wayar Android (Android Applications) wa'danda graphic designers zasu iya yin ko wane irin ayyukansu dasu, kuma a ko a'ina suke.

Samun wani ilimi wanda zaka iya yin aikinshi a cikin wayarka ta hannu har a biyaka ku'din aikinka a wannan zamanin ba 'karamin nasara bace.

Da dama daga cikin mutane har yanzu basu tabbatar anayin graphic design da wayar hannu ba har ya inganta, saboda sun ganin abun kamar yana da wuya ace anyi.

A sannu zamuga yanda ake fani da wayar hannu wajen yin graphic design.





Post a Comment

0 Comments