Menene Coins kuma menene Tokens
Kasuwancin cryptocurrency na ci gaba da haɓaka kowace rana. Duk da wannan haɓaka datakeyi, ana samun ƙarin ruɗani kewaye da sharuɗɗan daban-daban a cikin masana'antar. Ɗayan irin wannan misalin shine bambanci tsakanin tsabar kuɗin crypto (coins) da alama (tokens). Zamuyi ƙoƙarin bayyana bambance-bambance masu mahimmanci tsakanin waɗannan ra'ayoyin biyu.
Video: banbancin coins da tokens👇👇
Coins sune cryptocurrency Wanda suke da block chain nasu nakansu wato hanyar kididdiga tasu takansu da kuma ajiye bayanai na transection nasu da kuma tsare su.
Misalan Coins sune :
(1) Bitcoin (BTC)
(2) Ethereum (ETH).
(3) Binance coin (BNB).
(4) Tron (TRX).
(5) Bitcoin (BTC).
Tokens sukuma basu da block chain nasu nakansu suna dogara ne da coins , kuma anasamar dasune daga wani block chain yayin da bukatar hakan tatashi.
Misalan Tokens sune :
(1) Bittorent (BTT) wanda aka Gina kan blockchain Na Tron.
(2) Smart key (SKY) Wanda aka Gina kan blockchain Na Ethereum.
(3) Trust wallet token (TWT) wanda aka Gina kan blockchain Na Binance.
Da sauran su.
BANBANCI TSAKANIN ERC20 , TRC20 , BEP2 DA KUMA BEP20.
*ERC20 : Shine token din da aka Gina kan blockchain Na Ethereum.
*TRC20 : Anginashi akan blockchain na Tron.B
*EP20 : Anginashi akan blockchain na Binance Smart chain.
*BEP2 : Anginashi akan blockchain na Binance coin *BNB
Blockchain na farko da aka fara dora Tokens akansa shine ERC20, daga baya aka fara akan BEP20 da kuma TRC20.
0 Comments