Gabatarwa
Cryptocurrency, wani lokacin ana kiransa crypto-currency ko crypto, wani nau'i ne na kuɗi da ke wanzuwa ta dijital Wanda yake amfani da cryptography don amintar ma'amaloli. Cryptocurrencies ba su da cibiyar bayarwa ko daidaitawa, maimakon yin amfani da tsarin da aka raba don yin rikodin ma'amaloli.
Kalmar Crypto asalin ta kalmar Girkawa ne (Greek Word), tana nufin "Secret" ko "Hidden", abin nufi "Sirrance" ko "Rufaffe", daga nan aka samo kalmar Crypto da ma'anar ta, dalilin da yasa aka ba ma kudin Internet wannan suna shine saboda tsarin yadda aka shirya kimiyyar gudanar dashi, akan wani tsari da ake ce ma "Block Chain Technology", ko "Kimiyyar da take jere akan tsari hawa-hawa kamar bulo".
Tsarin Crypto Currency, yana kan abinda ake ce ma Block Chain Technology ne, shi kuma block chain Technology tsari ne na Database, duk wanda yasan me ake kira da database toh zai yi saurin fara hasaso wannan kimiyyar ta Block Chain.
Kalli wannan videon👇👇👇
Database wuri ne ko tsari ne da ake ajiye bayanai, da tattara su wuri guda ko a rarrabe, tare da canza su ko gyara su a lokacin da ake bukata.
Tsarin database yana da yawa, yafi guda 40 a bangaren masu ilimin Computer, akwai Distributed database, akwai Relational database, akwai Centralized, akwai decentralized, akwai Cloud da sauran su.
Toh shi Block Chain Technology yana kan tsarin Decentralized distributed ledger ne, sai dai tsarin sa yasha ban ban da asalin tsarin database ta wasu wurare, shi Block Chain Technology an tsari ne ta yadda ba'a iya canza bayanan dake cikin sa da zaran an shigar, kuma ba'a iya sace shi, ko hacking din sa ko ayi masa kutse saboda tsaron da aka saka masa.
Har yau an gagara samun wani ko wasu kwararrun hackers da suka iya hacking din Block Chain Technology, ba'a samu ba, hatta wadanda suka fi kowa kwarewa a harkar Internet da suke kasar Switzerland da Japan da Uruguay sun sadakar cewa ba zasu iya komai ma Block Chain Technology ba, wato ginin Mahdi ka ture kenan.
Shi Block Chain Technology baya karban komai sai dai dai da tsarin sa, toh idan ya karba kuma babu wanda zai iya dakatar dashi har wanda ya kirkiro tsarin.
Haka zai yi ta tafiya duniya tana amfana dashi Koda masu shi sun mutu ko sun watsar dashi.
Misali, koda wanda ya kirkiro Bitcoin yace ya fasa ya daina, toh a yau ba zai iya dakatar dashi ba, sai dai ya hakura.
Haka kuma tsarin Block Chain Technology yana iya detecting wanda yayi attempt zai shige shi da wrong information, kuma ya dakatar da mutum na har abada daga shiga tsarin domin 'dora Coin ko wani information.
Sannan ba'a iya kwace shi zuwa hannun mutum guda, saboda an gina Block Chain Technology ne akan tsaron da wani 'dan Adam ba zai iya canza shi ba.
Kuma baya karkashin kulawar wata kasa ko wata gwamnati ko wani mutum, wannan shine babban dalilin gwamnatocin kasashe na yaki da Block Chain Technology, saboda basu da iko dashi.
Toh sai dai asalin tsarin Block Chain Technology ba anyi shine saboda harkar kudi ba zalla.
A'a anyi shi saboda duk wata harkar ajiye bayanai ta Online ne a duniya, sai dai harkar kudin Crypto Currency ta sanya mutane da dama basu san cewa block chain Technology bai tsaya akan harkokin kudi kadai ba.
Menene Crypto currency?
cryptocurrency ana kiranshi da kuɗin dijital ne wanda aka tsara don amfani da shi akan intanet.
Bitcoin, wanda aka ƙaddamar a cikin 2008, shine farkon cryptocurrency, kuma ya kasance mafi girma, mafi tasiri, kuma sananne.
A cikin shekaru goma tun lokacin, Bitcoin da sauran cryptocurrencies kamar Ethereum sun girma azaman madadin dijital zuwa kuɗin da gwamnatoci suka bayar.
Sai dai, kafin a fara wannan harkar Crypto currency a yau, tun da dadewa, wuraren 1980s, masana harkokin internet suke ganin ya dace duniya ta samar ma kanta da harkokin kudaden da ba'a iya ganin su, kuma ba'a iya taba su.
Saboda cigaba da amfani da kudaden takarda yana 'kara karya tattallin arziki duniya.
Ta yadda gwamnatoci suke kashe kudade masu yawa wurin buga su, da kashe kudade masu yawa wurin kula dasu idan sun yage ko sun 'koke ko sun lalace, sannan ana saurin sace su da gano inda suke da wanda yake dasu.
Wannan yana daga cikin a baben da suka sa manyan masana ganin an kawo karshen wannan matsalar.
Tun daga lokacin da aka fito da tsarin transfer din kudi ta waya, daga Account din mutum na banki zuwa wani banki masana suka tabbatar da cewa tsarin Block Chain Technology zai yi nasara.
Kuma hakan aka yi, gashi yayi nasara.
Har wa yau, tun shekarun baya masu kokarin kwato 'yancin 'dan Adam suna cewa ya kamata ace a yanzu mutane sun samu "Financial Freedom" wato " 'Yancin gashin kai ta bangaren harkokin kudi", ba sai sun jira wata kasa ko wata gwamnati ta amince da kudi kaza ba.
Suna cewa saka bakin gwamnati acikin harkar kudi yana danne cibagan duniya da walwalar mutane.
A shekara ta 2008, "Satoshi Nakamoto" masanin harkar internet kuma 'dan rajin neman Financial Freedom a duniya, yayi nasarar kera kudin Online, kuma ya saka masa suna "Bitcoin".
Bayan ya kammala aikin a 2008, sai a 2009 ya qaddamar dashi, wanda shine yayi nasara a karon farko a tarihin duniya da har aka gagara dakatar dashi.
Kudin farko da aka samar shine "Bitcoin", an saka masa sunan ne saboda an gina lissafi na'urar juyawa kudin ne da lissafin Computer na salon Algorithm, wato shi Algorithm asalin wanda ya kirkiro wannan lissafin da Computer take kai wani babban Malamin Musulunci ne, sunan "Imam Jabir Bin Hayyan Al-Khawarizmi", shine Turawa suka boye sunan sa domin kada duniya tasan Musulmi ne suka kawo wannan tsarin lissafin na Computer.
Tsarin lissafin algorithm akan Computer yana bugawa ne da 'digo ko "Bit".
Toh daga nan suka saka sunan kudin Crypto currency na farko da "Bitcoin".
Amma a farkon lokacin da aka kirkiro shi yana Naira biyar, ko Naira goma a 2009, bayan shekaru 10 ya tashi daga Naira goma ya koma Naira miliyan 24 ko wane daya, misali: wanda ya sayi Bitcoin guda dari a 2009 a yau kana ganin nawa yake dashi? ai da yawa.
Bitcoin ba shine Crypto Currency ba, shi Bitcoin 'daya ne daga cikin kudaden da suke yawo online kuma ake amfani dasu, shi Bitcoin dai shine na farko, shine babba dan haka yafi kowane Coin tsada.
Misali:
Idan aka ce maka akwai kudaden Takarda a duniya (Fiat Currency) a duniya da yawa, toh kudin Nigeriya (Naira) ba itace kadai kudin da ake amfani da ita a duniya ba.
Akwai Riyal, akwai Dollar, akwai Cefa, akwai Ghana Cedi, akwai Pound, akwai Yuro da sauran su.
Toh haka ma Crypto currencies suke, akwai su da yawa sun fi dubu biyar akan Block Chain Technology na duniya, misali, akwai:
1. Bitcoin.
2. Etherium.
3. Core.
4. Binance (BNB).
5. Doge coins.
6. Tron (TRX).
7. Renec.
8. XRP,...
0 Comments